FA Cup: City za ta kara da Newcastle a quarter finals

FA Cup

Asalin hoton, Getty Images

Mai rike da FA Cup, Manchester City za ta ziyarci Newcastle United a wasan daf da na kusa da na karshe.

Arsenal wadda ta lashe FA Cup sau 13 za ta je Sheffield United, ya yin da Chelsea wadda rabon ta da FA Cup tun 2018 za ta ziyarci Leicester City.

Daya wasan na Quarter finals shi ne wanda Norwich City za ta jira wadda ta yi nasara tsakanin Derby ko Manchester United domin karawa da ita.

Za a buga wasannin ne a karshen mako na 21 da 22 ga watan Maris.

Manchester City mai rike da kofin ta kawo wannan matakin. bayan da ta doke Sheffield Wednesday mai buga Championship da ci 1-0.

Tuni dai City ta lashe Caraboa Cup a karshen mako, bayan da ta yi nasara a kan Aston Villa da ci 2-1 a Wembley.

Newcastle United mai FA Cup shida ta dolke West Brom ne da ci 3-2 shi ne ta kawo zagayen quarter finals a karon farko tun 2006.

Arsenal ce ta farko da ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a bana, bayan da ta ci Portsmouth mai buga League One.

Sheffied United kuwa doke Readind ta yi 2-1 ta zo wannan matakin da rabon ta da shi tun 2014.

Chelsea kuwa ta yi namijin kokari da ta fitar da Liverpool da ci 2-0 ranar Talata, ita kuwa Leicester City cin Birmingham ta yi 1-0, kuma Ricardo Pereira ne ya ci mata kwallon daf da za a tashi karawar.

A karon farko Norwich City ta kai zagayen quarter finals tun 1991/92, bayan da ta yi nasara a kan Tottenham da ci 3-2 a bugun fenariti, yayin da suka tashi wasan 1-1 har da karin lokaci.

Jadawalin FA Cup karawar quarter finals

  • Sheffield United da Arsenal
  • Newcastle da Manchester City
  • Norwich da Derby/Manchester United
  • Leicester City da Chelsea