An ci tarar Ancelotti, bayan amsa laifin rashin da'a

Ancelotti

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ci tarar Carlo Ancelotti fam 8,000, bayan da ya amsa tuhumar rashin da'a a lokacin buga gasar Premier.

An bai wa kocin na Eveton jan kati a ranar Lahadi a wasan da suka yi 1-1 da Manchester United a Goodison Park.

Dan kasar Italiya ya kalubalanci alkalin wasa Chris Kavanagh, bayan da aka soke kwallon da Dominic Calvert Lewin ya ci da cewar an yi satar gida.

Ancelotti ya zama koci na farko da aka bai wa jan kati a lokacin gasar Premier.

Bayan da Ancelotti, mai shekara 60, ya amsa laifinsa ne ya hana a yanke hukuncin dakatar da shi.