Ighalo ya kai Man United quarter finals a FA Cup

Odion Ighalo

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a FA Cup na bana, bayan da ta doke Derby County ranar Alhamis.

United ta fara cin kwallo ta hannun Luke Shaw, saura minti hudu a je hutu Odion Ighalo ya kara na biyu.

Dan wasan na tawagar Najeriya shi ne ya ci na uku saura minti 20 a tashi wasan kuma na biyu a ranar, sannan na uku da ya ci a United kawo yanzu.

Da wannan sakamakon United za ta fafata da Norwich City a wasan daf da na kusa da na karshe.

Sauran wasannin quarter finals din Sheffield United da Arsenal, Newcastle da Manchester City da wasa tsakanin Leicester City da Chelsea.

Za a buga wasannin ne a karshen mako na 21 da 22 ga watan Maris.

Kungiyar ta Old Trafford tana ta biyar a kan teburin Premier da maki 42 da tazarar maki uku tsakaninta da Chelsea ta hudu.

United za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan mako na 29 a gasar Premier ranar Lahadi.

Kungiyoyin na Manchester sun fafata sau uku a kakar bana, inda United ta ci 2-1 ranar 7 ga watan Disamba a gasar Premier a Etihad.

A ranar 7 ga watan Janairu, City ta yi nasarar cin 3-1 a League Cup a Old Trafford a wasan farko.

Sai dai a wasa na biyu na Caraboa da suka yi a Etihad ranar 29 ga watan Janairu, United ce ta ci 1-0.

Bayan karawa da City, United za ta ziyarci LASK Linz ranar 12 ga watan Maris, domin buga gasar Zakarun Turai ta Europa League.

Daga nan ne United za ta ziyarci Tottenham a gasar Premier fafatawar mako na 30 ranar 15 ga watan Maris.