Makomar: Kokcu, Calvert-Lewin, Magalhaes, Edouard, Ighalo da Ceballos

Orkun Kokcu

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta fara tattaunawa kan dan wasan Feyenoordda take son ware wa fam miliyan £23 domin karbo Orkun Kokcu, mai shekara 19. (Mail)

Everton na tattaunawa da Lillekan dan wasan tsakiya na Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, wanda Arsenal da Tottenham suna nuna sha'awa a Janairu. (Independent)

Everton kuma na son dan wasan CelticOdsonne Edouard, mai shekara 22, inda ta ke sa ido kan dan wasan dan kasar Faransa mai shekara 21. (Mail)

Akwai yiyuwarManchester Unitedza ta saye dan wasan Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, da ta karbo aro daga Shanghai Shenhua, ta China zuwa Old Trafford. (Mail)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya karyata Rahotannin da ke cewa ya tuntubi Real Madrid da nufin kokarin sayen dan wasan Spain na tsakiya Dani Ceballos, mai shekara 23. (Marca)

Chelsea na tunanin karbo golan TrabzonsporUgurcan Cakir mai shekara 23 wanda rahotanni suka ce Liverpool na sha'warsa domin maye gurbin Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25. (Fotospor, via Express)

Dan wasan gaba na Ingila Jadon Sancho ya yi watsi da tayin fam £30,000 duk mako a Manchester City.(Mail)

Tottenham a shirye take ta kulla sabuwar yarjejeniya da dan wasan tsakiya Oliver Skipp, mai shekara 19, sabuwar yarjejeniya. (Football Insider)

Arsenal na sa ido kan dan wasan Gentdan kasar Canada Jonathan David, mai shekara 20. (Goal)

Hukumar kwallon Faransa ta samu takarda daga Paris St-Germain da ke tabbatar da cewa ba ta son dan wasanta Kylian Mbappe, mai shekara 21, ya tafi wasannin Olympics a Japan. (ESPN)

Arsenal da Everton dukkaninsu sun gaza sayen dan wasan Napolina Belgium Dries Mertens, mai shekara 32. (Star)