Golan Liverpool Alisson ba zai buga karawa da Atletico ba

Alisson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alisson ya koma Liverpool a kan £66.8m a watan Yulin 2018

Golan Liverpool Alisson ba zai buga fafatawar da za su yi da Atletico Madrid ranar Laraba ba a wasan 'yan 16 na Gasar cin Kofin Zakarun Turai saboda raunin da ya ji a kugunsa.

Kazalika Alisson ba zai buga karawar da za su yi da Bournemouth ba a gasar Firimiya ranar Asabar yayin da kuma ake shakkar ko zai shiga wasan da za su yi da Everton ranar 16 ga watan Maris.

Liverpool za ta karbi bakuncin Atletico ranar Laraba inda suka tashi da ci 1-0 a wasansu na farko.

Kocin Jurgen Klopp ya ce dan wasan mai shekara 27: "Ba zai buga wasan da za mu yi gobe da wanda za mu yi makon gobe ba."

"Bamu kammala nazari kan yanayin da yake ciki ba. Za mu yi hakan bayan mun samu hutu dari bisa dari."

Alisson, wanda ya buga wa Liverpool wasa 28 a kakar bana, ya yi raunin ranar Talata kafin karawar da suka yi ranar Talata wacce Chelsea ta doke su da 2-0 a zagaye na biyar na gasar cin kofin FA

Dan wasan dan kasar Brazil - shi ne dan wasa mafi tsada a duniya lokacin da ya koma Liverpool daga Roma a 2018 a kan £66.8m - kuma bai buga wasa tara ba a farkon kakar wasa sakamakon raunin da ya ji a wasansu na farko da Norwich City a watan Agusta.

"Shi [Alisson] ya samu wata tangarda lokacin atisaye kafin wasan da muka yi da Chelsea," in ji Klopp.

"Dukkan mu mun yi tsammanin babu abin da ya same shi amma yanzu a bayyane yake ba zai buga wasan ba. Mun tsara cewa ya zauna a benchi .

"[An yi masa gwaji] washegari inda aka gano wani abu, don haka yanzu ba zai yi wasa ba."