Makomar De Bruyne, Sterling, Skriniar, Zidane, Cantwell, Nani da Matic

Manchester City's Kevin de Bruyne

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Manchester City na son sabunta kwangilar Kevin de Bruyne da Raheem Sterling

Manchester City a shirye ta ke ta sabunta kwangilar 'yan wasanta biyu Kevin De Bruyne, mai shekara 28 dan kasar Belgium, da dan wasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 25. (Mail)

Manchester City na son sake taya dan wasan baya na Inter dan kasar Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25, bayan ta taya shi kan fam miliyan £52. (Calciomercato - in Italian)

Juventus a shirye ta ke ta ware wa kocin Real Madrid Zinedine Zidane fam miliyan £7 domin dauko tsohon dan wasanta matsayin koci a karshen kaka. (Mail)

Tottenham za ta yi hamayya da Liverpool da Manchester United kan dan wasan Norwich Todd Cantwell dan kasar Ingila mai shekara 22. (Express)

Manchester United ta ki amincewa ta tsawaita kwangilar shekara daya kan dan wasanta mai shekara 31 dan kasar Serbia Nemanja Matic, dan wasan da kwangilar shi ke dab kawo wa karshe. (Manchester Evening News)

Chelsea na tattaunawa kan dan wasan VfL Bochum mai shekara 18 Armel Bella-Kotchap. (Sun)

Dan wasan Chelsea dan kasar Faransa Olivier Giroud, mai shekara 32, da ake alakantawa da Inter Milan, yanzu yana son ci gaba da taka leda a Stamford Bridge. (Evening Standard)

Tsohon dan wasan Manchester United Nani ya shaida wa dan wasan Portugal Bruno Fernandes zai fi son ya komawa Old Trafford maimakon Manchester City idan har zai bar Sporting Lisbon. (Star)

Bayern Munich da Borussia Dortmund dukkansu na son dan wasan baya na Belgium Thomas Meunier, mai shekara 28, idan kwangilar da Paris St-Germain ta kare a karshen kaka. (Goal.com)

Dan wasan gaba na Chelsea Tammy Abraham yana son dawo wa taka leda a wannan watan bayan ya murmure daga raunin da ya ji tare da fatan buga wasan sada zumunci da Ingila za ta buga tsakaninta da Italiya da kuma Denmark. (Evening Standard)