Yadda Coronavirus ta addabi duniyar wasanni

Filin wasa na San Paolo

Asalin hoton, AFP/CIRO FUSCO/ANSA

Bayanan hoto,

Italiya ta umarci duk wasu manyan wasanni a buga su ba tare da 'yan kallo ba har zuwa 3 ga Afrilu, ciki har da wannan filin wasan na Napoli - San Paolo

Yayin da annobar cutar nimfashi ta coronavirus ke ci gaba da karade sassan duniya, mahukunta na ci gaba da sokewa da dagawa ko kuma buga wasanni ba tare da 'yan kallo ba.

Ga yadda cutar ke shafar harkoki a duniyar wasanni a takaice:

  • Tun a makon da ya gabata ne aka dage wasan hamayya tsakanin Juventus da AC Milan a gasar Copa Italia saboda tsoron yaduwar cutar.
  • Wasannin Zakarun Turai tsakanin Valencia da Atalanta a Champions League da kuma Inter Milan da Getafe a Europa za a buga su ne ba tare da 'yan kallo ba.
  • Wasa tsakanin Paris St-Germain ta Faransa da Strasbourg ya samu tsaiko saboda tsoron yada cutar.
  • An dage wasanni da dama a Serie A ta Italiya da gasar kasashen Switzerland, China, Japan, Koriya ta Kudu.
  • Kulob din Brondby na kasar Denmark ya killace mutum 13 bayan an gano tsohon dan wasan kasar Thomas Kahlenberg yana dauke da cutar.
  • Har yanzu ana dari-dari game da yadda gasar Olympics za ta gudana a Tokyo na Japan.
  • Tauraron dan wasan kwallon kwando LeBron James ya ce ba zai buga wasa ba idan har hukumar NBA ta ce ba za a yi da 'yan kallo ba.
  • Tuni NBA din ta umarci kulob-kulob da su nemo hanyar da za su buga wasannin ba tare da 'yan kallon ba.
  • Wasan Zari Ruga na Six Nations na mata tsakanin kasashen Scotland da Faransa an dage shi saboda wata 'yar wasa ta kamu da cutar.
  • Ita ma gasar Chinese Grand Prix ta tseren motocin Formula One an dage ta, wadda aka shirya gudanarwa ranar 19 ga watan Afrilu a Shanghai.