Premier League: Liverpool ka iya lashe kofi a wasa uku nan gaba

Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mohamed Salah ne ya farke kwallo daya

Liverpool ta farfado daga kwallon da Bournemouth ta cilla mata kuma ta cinye wasan a kokarinta na lashe kofin Premier na farko cikin shekara 30.

Nasarar na nufin Liverpool ka iya lashe kofin nan da ranar 16 ga watan Maris, sanda za ta yi wasa da Everton - idan Manchester City ba ta ci wasanta uku ba tsakaninta da Man United da Arsenal da Burnley.

Sakamakon ya sa tawagar Jurgen Klopp ta bayar da tazarar maki 25 ga Man City - ta biyu a teburi.

City da United za su fafata a wasan hamayyar Manchester ranar Lahadi a filin wasa na Old Trafford da karfe 5:30.

An fara cin Liverpool ne ta hannun Callum Wilson bayan Jefferson Lerma ya kawo kwallo. Kwallon ta jawo ce-ce-ku-ce saboda an tunkude Joe Gomez kafin a ci.

Mohamed Salah ne ya farke, wanda ya buga wa Liverpool wasa na 100 a Premier.

Sadio Mane ya kara ta biyu bayan Virgil van Dijk ya garo kwallo amma fa sai da James Milner ya tsige wata kwallo daga kan layi - ba don haka ba da canjaras za a yi.

Wasa uku na gaba da Liverpool za ta yi sun hada da Everton da Crystal Palace da Man City.