Makomar Henderson, Ter Stegen, Skriniar, Abraham, Matic, Stones da Zidane

Henrikh Mkhitaryan

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea na son dauko golan Sheffield United dan Ingila Dean Henderson, 22, wanda Manchester United, ta karba aro domin magance matsalarta da tsaron gida. (Star on Sunday)

Chelsea kuma na tunanin dauke golan Jamus Marc-Andre Ter Stegen, mai shekara 27, idan har ya yanke shawarar barin Barcelona a bazara. (Sunday Express)

Kocin Manchester City Pep Guardiola a shirye yake ya ware fam miliyan £80 kan dan wasan baya na Inter Milan dan kasar Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25, a kokrinsa na magance matsalar tsaron gidansa. (Sunday Express)

Dan wasan gaba na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 22, ya ki amincewa da tayin Chelsea. (Sunday Mirror)

Dan wasan tsakiya dan kasar Serbia Nemanja Matic, mai shekara 31, zai sabunta kwangila domin tsawaita zaman shi a Manchester United.(Manchester Evening News)

Kocin Arsenal Mikel Arteta zai ci gaba da farautar dan wasan baya na Manchester City John Stones, mai shekara 25. (Team Talk)

Tsohon dan wasan Juventus Zinedine Zidane ya yi ikirarin cewa kulub din bai tuntube shi ba kan rahotannin da ke cewa zai koma horar da Juve idan kwangilar shi ta kawo karshe a Real Madrid. (Goal.com)

Inter na son sayen dan wasan Tottenham dan kasar Belgium Jan Vertonghen, mai shekara 32, a wannan bazarar. (SempreInter)

Everton na cikin kungiyoyin da ke sha'awar dan wasan baya na Manchester City Tosin Adarabioyo, mai shekara 22, wanda Blackburn ta karba aro. (90 Min)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce dan wasan Armenia Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 31, da Roma ta karba aro zai iya dawo wa Emirates.(Evening Standard)

Arsenal na sa ido kan dan wasan Aston Villa dan Ingila Jaden Philogene-Bidace, mai shekara 17. (Birmingham Mail)