Premier League: Wasan hamayyar Manchester mako na 29

Wasan hamayyar Manchester

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Da misalin karfe 5:30 agogon Najeriya za a yi fafatawar a filin wasan na Old Trafford

Ana sa ran dan wasan Manchester United Harry Maguire zai iya warkewa daga ciwon da yaji a idon sahunsa yayin atisaye.

Axel Tuanzebe ya kara warkewa daga ciwon da ya ji, amma Daniel James da Aaron Wan-Bissaka ba su yi atisaye ba wannan makon kuma za a duba lafiyarsu.

Har yanzu akwai shakkun ko Kevin de Bruyne zai warke daga ciwon bayansa wanda ya hana shi buga wasan Manchester City da ta samu nasara kan Sheffield a ranar Laraba.

Pep Guardiola ya ce, "Kevin de Bruyne ba ya jin dadi amma yana samun sauki".

Bayani kan wasan hamayya tsakanin Manchester United da Manchester City:

Manchester United

 • United za ta iya rashin nasara sau hudu a jere a gida a hannun City a duka gasannin da suka hadu, wanda wannan ne karo na biyu da hakan zai iya faruwa a tarihi.
 • City da za ta je bakunci ta yi nasara sau shida cikin wasa bakwai da aka buga a baya a duka gasanni.
 • United na kokarin cinye City sau biyu a jere a Premier a karon farko tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi murabus.
 • United ta ci wasa shida ta yi canjaras uku a wasa tara da ta yi a duka gasannin da take bugawa.
 • Ta yi wasa bakwai ba a zira mata kwallo ba cikin wasa takwas, ta ci kwallo 22 an kuma zira mata biyu.
 • Tun farkon fara wasannin wannan kakar, babu wani dan wasa da yayi kuskuren da ya janyo aka ci kungiyarsa a Premier sama da golan United wato David de Gea wanda ya yi hakan sau bakwai.
 • Kwallo 33 City ta zira wa dan asalin Spaniyan a Premier, kwallo mafi yawa kenan sama da duk wani abokin hamayyarta.

Manchester City

 • City ta ci wasanninta hudu da ta buga a bayan nan a duka gasar da take bugawa, kama daga Premier da Lig Cup da Champions da kuma FA.
 • Ta yi rashin nasara ne sau daya kacal cikin wasa takwas da ta buga a bayan nan, ta yi nasara a shida ta kuma yi canjaras a daya.
 • City ba ta taba rashin nasara a Premier ba a watan Maris karkashin Pep Guardiola, rashin nasara na karshe da ta yi shi ne wanda Manchester United ta doke ta a 2016.
 • Guardiola ya ci wasa ukun karshe da ya je Old Trafford a Premier, babu wata kungiya da ta yi sama da haka a Premier.
 • Segio Aguero ya ci kwallo tara a duka gasar da aka yi wasan hamayyar Manchester.