Premier League: Chelsea ta zazzaga wa Everton kwallaye

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Olivier Giroud ne ya cike wa Chelsea kwallo ta hudu da ta ci

Chelsea ta yi wa Everton ruwan kwallaye kuma tana ci gaba da rike matsayinta na hudu a teburin Premier.

Chelsea ta fara zira kwallo ta farko ne ta hannun matashin dan wasanta Mason Mount a minti na 14 da fara wasan.

A minti na 21 ne dan wasan gaban Sifaaniya Pedro ya zira kwallo ta biyu, wanda hakan ya kara bai wa Chelsea kwarin gwiwa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci dan wasan gefe na Chelsea dan Brazil, Willian ya kara ta uku a minti na 51.

Minti uku tsakani dan wasan gaban Faransa Olivier Giroud ya kara ta hudu.

Cikin wasa 24 da Everton ta buga a Stamford Bridge a Premier ba ta yi nasara ko daya ba - ta yi canjaras 11 ta yi rashin nasara 13.

Tun daga washegarin ranar Kirsimati da Carlo Ancelotti ya karbi Everton ya fi kowanne kulob samun maki, inda ya samu 18 - Liverpool da ta hada 30 da Manchester City mai 19 ne kawai suka fi shi.

Yanzu dai Chelsea za ta ziyarci Aston Villa a ranar Asabar mai zuwa, yayin da Everton za ta buga wasan hamayya da Liverpool.