Dan wasan Nassarawa United ya mutu ana tsaka da wasa

Kwallon Firimiyar Najeriya

Asalin hoton, NPFL

Bayanan hoto,

Nassarawa ce ta casa Katsina United a wasan da ci 3-0

Dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United, Martins Chinenye ya fadi ana tsaka da wasa, wanda hakan ya kai ga mutuwarsa.

Kusan minti na 40 ne da fara wasan dan wasan ya yanke jiki ya fadi, kamar yadda kocin kungiyar ya tabbatar wa da BBC.

Ita ma hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya wato LMC ta tabbatar da faruwar lamarin.

Rahotonni su ce dan wasan bai kai ga mutuwa ba har na wani tsahon lokaci, yayin da aka kwashe mintuna wurin kunna motar asibiti amma ta ki tashi.

Karshe dai an fitar da dan wasan a wata motar ta daban maimakon ta asibitin da aka tanada.

Ana kammala wasan ne aka bayyana wa abokan wasan marigayin cewa ya rasu.

Wannan ne wasan mako na 23, inda aka tashi wasan Nassarawa United na da 3 Katsina United na nema.