Premier League: Man United ta casa Man City a wasan hamayya

United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Scott McTominay ne ya ci kwallo ta biyu a Old Trafford

Manchester United ta doke Manchester City da 2-0, sai dai tana nan a matsayi na biyar a teburin Premier.

Wannan ce nasara ta biyu da United ta yi a kan City a jere a Premier a karon farko tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi murabus.

Anthony Martial ne ya fara jefa kwallo ta farko a minti na 30, kuma kwallo ta 11 kenan da ya zira a gasar ta bana.

Martial ne dan wasan da ya fara cin kwallo sau uku a wasan hamayyar Manchester a jere tun bayan Eric Cantona a 1993 da kuma 1996.

Sergio Aguero ya zira kwallo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sai dai an hana kwallon saboda ya yi satar gida.

Scott McTominay ya kara kwallo ta biyu a karshen lokaci bayan kuskuren da golan City Ederson ya yi.

United za ta buga wasanta na gaba a Premier da Tottenham, inda za ta je bakunci gidan tsohon kocinta Mourinho.