Juventus ta cinye Inter Milan ta koma ta daya a teburi

Juventus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Juve ta koma ta daya kan teburi da maki daya

Juventus ta doke Inter Milan kuma ta haye teburin gasar Serie A - a wani wasa da aka buga ba tare da 'yan kallo ba.

Wannan na daya daga cikin manyan wasannin kwallon kafa a kakar wasa ta bana a Italiya, kuma za a ci gaba da buga wasannin babu 'yan kallo a filayen wasan har 3 ga watan Afrilu.

Aaron Ramsey da Paulo Dybala ne suka zira kwallon da da ta baiwa Juve damar darewa kan teburin da maki daya saman Lazio.

Da alamun kalubalen gogayyar da Inter ke fama da shi ya zo karshe tun da abokiyar hamayyarta Juve ta ba ta maki 9 tsakanin kungiyooin biyu.

Cristiano Ronaldo bai ci kwallo ba a wasan, wanda karon farko ke nan hakan ta faru a gasar Serie A tun 10 ga watan Nuwambar bara.

Kawo yanzu mutum 366 suka mutu a Italiya dalilin cutar Coronavirus, kuma akwai mutum 7,375 da suka kamu da ita.