Coronavirus: Minista ya kira shugabnnin Gasar Serie A 'masu taurin kai'

Parma v SPAL

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An buga wasan Parma da SPAL ne ba tare da 'yan kallo a cikin filin wasan ba

Ministan wasanni na Italiya ya tuhumi manajojin gasar Serie A da kasancewa masu masu taurin kai bayan sun yi watsi da kiran da yayi na dakatar da gasar saboda coronavirus.

Tun da farko, Vincenzo Spadafora ya ce hankali ma ba zai dauka ba idan aka ci gaba da buga wasannin kwallon kafa bayan da aka killace mutum miliyan 16 a kasar ta Italiya.

Amma an ci gaba da buga wasannin a karkashin gasar ta Serie A a ranar Lahadi, sai dai babu 'yan kallon da aka bari suka shiga filayen wasan.

Minista Spadafora ya ce: "Duniyar kwallon kafa na ganin ta fi karfin dokoki da sadaukar da kai".

Yayin da yake hira da tashar talabijin mallakin gwamnati ta RAI, ya kara da cewa: "A yau an buga wasanni saboda taurin kan Gasar Serie A da shugabanta Paolo dal Pino."

"Muna ba 'yan Italiya shawara da su zauna a gidajensu."

A makon jiya, gwamnatin Italiya ta sanar da cewa za rika buga dukkan wasannin a cikin filayen wasan da babu 'yan kallo cikinsu sam-sam har zuwa ranar 3 ga Afrilu.

An buga wasannin kamar na Parma da SPAL. Wannan wasan an fara shi ne bayan jinkirin minti 75, kuma bayan da Spadafora ya mika umarnin nasa.

An kuma buga wasu wasanni hudu ba tare da 'yan kallo sun shiga filayen wasannin ba. Cikinsu Juventus ta buga da Inter Milan.

Ana kuma sa ran Sassuolo za ta buga wasa tare da Brescia ranar Litinin duk da halin da ake ciki.

Kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Italiya, AIC ta fitar da wata sanarwa bayan da aka kammala wasan Parma da SPAL, wanda a cikinta ta soki matakin ci gaba da buga wasannin na Lahadi.

Amma a nasu bangaren masu kula da gasar kwallon kafa a kasar, Lega Serie A sun ce tun farko sun bi tsarin da aka amince da shi ne na hana 'yan kallo shiga filayen wasa.

Sanarwar ta kuma soki hukumomin kasar da kungiyar 'yan wasan kwallon kafa ta Italiya da yin katsalandan gabanin wasan da aka buga tsakanin Parma da SPAL.