Bauchi: Kaura na zargin Isa Yuguda da M.A da salwantar da tiriliyan daya

Bauchi Governor Bala Muhammad

Asalin hoton, Bauchi State Government

Bayanan hoto,

Gwamnan Bauchi Bala Kaura

Kwamitin da gwamnatin jihar Bauchi da ke Najeriya ta kafa domin bin diddigi da karbo kadarorin gwamnati da ake zargin an wawure, ya yi zargin cewa an salwantar da kudi fiye da naira tiriliyan daya.

Kwamitin ya ce a zamanin tsofofin gwamnonin jihar biyu wato Malam Isa Yuguda da kuma Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ne kudaden suka salwanta.

Mutanen biyu sun yi mulki a lokuta daban-daban daga 2007 zuwa 2019.

Kwamitin ya ce ko da yake ya yi nasarar karbo motoci masu yawan gaske da wasu kadarori, to amma har yanzu ya kasa bambaro fiye da naira tiriliyan daya daga gwamnatocin biyu da suka shude.

Tsofofin gwamnoni biyu, Isa Yuguda da Muhammad Abdullahi Abubakar ne suka jagoranci gwamnatin jihar daga 2007 zuwa 2019.

Don haka kwamitin ke bukatar tsofaffin jami'an gwamnatin su maido kudaden da ake zargin sun wawure.

Malam Musa Azare shi ne mataimakin kakakin kwamitin, ya yi bayani kan abin ta'ajibi da suka bankado yayin aikinsu na watanni takwas.

"Akwai abubuwa da dama da muka gano daga kwangiloli da aka bayar da su."

Ya kara da cewa: "Ko dai an bayar da su amma ba a yi ba bayan an fitar da kudadensu, ko kuma an yi su rabi-da-rabi. Ko ma an bayar da su kan kudaden da ake zargin sun yi yawa."

Ya ce sun kira 'yan kwangilan da suka aiwatar da wadannan ayyukan domin su gano ainihin gaskiyar lamarin.

"Wasunsu sun amsa kiran kuma sakamakon bayanan da suka bayar ne ma aka saka cikin wannan rahoton binciken," in ji shi.

Cikin wadanda kwamitin ya kara har da wasu jami'an gwamnatocin da suka gabaci wannan.

Martanin tsofaffin gwamnatocin

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Gwamnatocin biyu da suka shude a jihar Bauchi sun fito suna musanta zargin wawure sama da naira tiriliyan dayan da wannan kwamitin binciken ya yi musu.

Alhaji Salisu Ahmad Barau Tafawa Balewa, shi ne mai magana da yawun tsohuwar gwamnatin jihar ta Malam Isa Yuguda, wanda ya yi gwamna daga 2007 zuwa 2015.

Ya ce "In mai fadar magana wawa ne, ai mai jin ta ba wawa ba ne. Gwamantin Isa Yuguda karkashin jam'iyyar PDP a wancan zamanin ta sami jimillar kusan Naira biliyan 600 ne."

Ya kara da cewa cikin biliyan 600, gwamnatinsu ta kashe kimanin biliyan 500 ne wajen biyan albashin ma'aikata da sauran ayyuka na yau da kullum.

"Saura kuma ne Isa Yuguda ya yi tsimi da dabara har ya yi manyan ayyuka a jihar Bauchi kamar filin jirgin sama da jami'ar jihar, da kuma asibitin kwararru da sauran su."

Shi ma tsohon gwamnan jihar Barista Abdullahi Abubakar da ya yi mulki jihar daga 2015 zuwa 2019, cewa ya ke yi bita-da-kullin siyasa kawai gwamnatin Bala Kaura ke yi masu.

Malam Ali M Ali shi ne mai magana da yawun tsohon gwamna M. Abubakar.

Kakakin na tsohon gwamna ya kuma ce batun da masu mulkin jihar na yanzu ke yi, wata dabara ce ta kawar da hankali daga zarge-zargen rashawa kan jami'an gwamnatin yanzu.

"Gaba daya kudaden da aka samu a shekara biyar ba su kai biliyan 350 ba. Alkaluman suna nan. Ina aka samo batun tiriliyan? Hankali ba zai dauka ba."

Ya kuma zargi gwamnati mai ci ta Bala Muhammad, Kauran Bauchi da "gaza aiwatar da wani abin a zo a gani cikin watannin da suka sami kansu a mulkin jihar."

To amma kwamitin ganowa da sake karbo dukiyar gwamnatin na musanta zargin bita-da-kulli da kuma kokarin badda-bami.

Gwamnatoci biyu da suka gabata a jihar ta Bauchi - wadanda kwamitin ke zargi da karkatar da dukiyar jihar da ta kai sama da naira tiriliyan daya - su ma sun gudanar da irin wannan binciken a baya.

Su ma sun rika zargin gwamnatocin da suka gabace su da yin ruf da ciki da dukiyar talakawa, amma daga bisani sai aka ji shiru kan lamarin.