Za a buga wasan PSG da Dortmund ba tare da 'yan kallo ba

Parc des Princes

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Filin wasan da ke daukar mutum 48,000 zai kasance fayau babu kowa

Za a buga wasan na biyu na gasar zakarun Turai tsakanin Paris St-Germain da Borussia Dortmund a ranar Laraba ba tare da 'yan kallo ba, saboda cutrar Coronavirus.

'Yan sandan birinin Pari ne suka yanke wannan hukunci a yau Litinin, domin takaita yaduwar cutar nunfashin.

PSG da ta lashe Lig 1, an zira mata kwallo 2-1 a wasan farko na Champions, kuma ita ce za ta karbi bakuncin kulob din kasar Jamus a filin wasa na Parc des Princes.

Paris St-Germain ta ce tana yin duk abin da ya kamata domin tabbatar da an buga wasan cikin yanayi mai kyau.

Ya zuwa yanzu an tabbaatr da mutane 1,116 wadanda ke dauke da wannan cuta a kasar Faransa.

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana China da Koriya ta Kudu da Italiya da kuma Iran ne kawai suke gaba da Faransa a kasashen da ke fama da cutar.