An dakatar da gasar Serie A saboda Coronavirus

Juventus da Inter

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ko a ranar Lahadi an buga wasa tsakanin Juventus da Inter Milan ba tare da 'yan kallo ba.

An dakatar da dukkan wasannin a kowanne mataki a Italiya har sai nan da 3 ga watan Afrilu mai zuwa, kamar yadda kwamitin shirya gasar Olympic na kasar ya sanar.

Ciki har da dukkan wasannin kwallon kafa na gasar Serie A, sai dai hakan bai shafi kulob Italiya ba da kuma kungiyoyin kasar da ke buga gasar kasa da kasa.

A baya an dakatar da zuwan 'yan kallo filin wasannin har sai uku ga watan Afirulun.

Ko a ranar Lahadi an buga wasa tsakanin Juventus da Inter Milan ba tare da 'yan kallo ba.

"Ba a taba fuskantar irin wannan yanayin ba dai a tarihi," inji kwamitin.

Gwamnatin Italiya na bukatar wata dokar Firaminista da za ta tabbatar da wannan hukunci, inji kwamitin.

Kwamitin Olympic na kasar yayi wata tattunawa da hukumar wasanni ta kasar ranar Litinin.

Italiya ce kasar Turai da wannan annoba ta munana a cikinta ya zuwa yanzu, inda mutane 7,000 suka kamu da sutar kuma tuni 3,00 suka mutu.