Manchester United za ta sayo Grealish da Bellingham, Lingard zai bar Old Trafford

Jack Grealish (left) and Jude Bellingham

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na shirin kashe £100m domin sayo dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Jack Grealish, mai shekara 24 da takwaransa na Birmingham mai shekara 16 Jude Bellingham a bazara. (Star)

Manchester United za ta sayar da dan wasan Ingila Jesse Lingard, mai shekara 27, a bazara. (Goal)

Dan wasan Chelsea dan kasar Brazil Willian, mai shekara 31, ya ce bai san makomarsa ba, a yayin da kwangilarsa ke shirin karewa a karshen kakar wasa ta bana sannan aka samu matsala game da batun komawarsa wata kungiyar. (Evening Standard)

Matar Willian Vanessa Martins ta ce mai yiwuwa mijinta na gab da kawo karshen zamansa na shekara bakwai a Chelsea. (Mirror)

Manchester United na kan gaba wurin son dauko dan wasan Borussia Monchengladbach da Switzerland Denis Zakaria, mai shekara 23. (Star)

Manchester City na da kwarin gwiwar cewa dan wasan Argentina Sergio Aguero, mai shekara 31, wanda ya fi kowanne dan wasanta zura kwallo, ba zai bar su a bazara mai zuwa ba, duk da haramcin da aka yi musu na buga gasar Zakarun Turai. (Evening Standard)

Barcelona na son sabunta kwangilar golan Jamus Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 27, kuma tana da kwarin gwiwar cewa zai amince da kwangilar duk da rade radin da ake yi cewa wasu kungiyoyi, ciki har da Chelsea, suna zawarcinsa. (Sport)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tsohon Zakaran damben boksin Floyd Mayweather ya nuna sha'awar sayen kungiyar Newcastle. (Newcastle Chronicle)

Mai yiwuwa Inter Milan ta sayo golan Bournemouth dan kasar Bosnia Asmir Begovic, mai shekara 32, wanda yanzu haka yake can AC Milan a matsayin aro, domin ya zama mataimakin Slovenian Samir Handanovic, mai shekara 35, a kakar wasa mai zuwa. (La Repubblica, via Sempre Inter)

Leeds ta bi sahun Southampton wurin zawarcin dan wasan Oxford Rob Dickie, mai shekara 24. (Football Insider)

Arsenal na ci gaba da sha'awar sayo dan wasan Paris St-German da Faransa Layvin Kurzawa, mai shekara 27. (France Football, via Sport Witness)

Dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Jamus Emre Can, mai shekara 26, ya bayyana cewa ya ki karbar tayin da kungiyoyi uku na gasar Firimiya suka yi masa na komawa can, ciki har da Manchester United, saboda biyayyar da yake yi wa tsohuwar kungiyarsa Liverpool. (Mail)

Dan wasan Manchester United Anthony Martial, mai shekara 24, ya ce zai mayar da hankali wurin shirin buga gasar Euro 2020 da za a yi a Faransa, amma bayan ya taimaka wa kungiyarsa wurin samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai. (RMC Sport, in French)

Dan wasan Leicester Jamie Vardy ya ce a shirye yake ya koma Ingila domin ya shiga tawagar da za ta buga mata agasar Euro 2020. Dan wasan mai shekara 33 ya yi ritaya daga buga gasar duniya bayan gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya da aka yi a 2018. (ESPN)