Da kyar Thibaut Courtois da Marcelo za su buga wasan Man City

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ta ci Real Madrid 2-1 har filin wasa na Bernabeu

Akwai fargabar 'yan wasan Real Madrid Thibaut Courtois da Marcelo ba za su buga wasa na biyu ba na Champions da za su yi da Manchester City ranar 17 ga watan Maris.

Mai tsaron ragar Belgium Courtois ya samu rauni ne a cinyarsa, yayin da dan wasan bayan Brazil Marcelo ya samu matsala a kafarsa.

Real Madrid ba ta ayyana lokacin da 'yan wasan za su warke ba, sai dai ta ce ana ci gaba da bibiyarsu su biyun.

Kungiyar da ta lashe Champions sau 13 za ta buga wasanta na gaba ne ba tare da kyaftin dinta ba Sergio Ramos, saboda jan katin da ya samu a wasan zagayen farko.

Manchester City ta doke Real Madrid da ci 2-1 har gida, ta hannun Gabriel Jesus da Kevin de Bruyne.