Bronze ce gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC a bana

BBC Women Footballer award Hakkin mallakar hoto BBC Sport

An bayyana Lucy Bronze a matsayin wadda ta lashe kyautar gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC ta shekarar 2020.

Bronze mai tsaron bayan tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila mai wasa a Lyon ta ci kyautar karo na biyu kenan, bayan bajintar da ta yi a 2018.

'Yar kwallon tawagar Netherlands da Arsenal, Vivianne Miedema ce ta yi ta biyu, sannan Megan Rapinoe mai taka leda a Reign 'yar Amurka ta yi ta uku.

Wannan ce kyautar da aka samu mutane da dama suka yi zaben a sashin BBC fiye da shekara shida da aka fara gudanar da kyautar.

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Sauran wadanda suka yi takarar sun hada da 'yar kwallon tawagar Australia da Chelsea, Sam Kerr da kuma 'yar Amurka mai wasa a Chicago Red Stars, Julie Ertz.

Bronze din ta karbi kyautar ce a gidanta da ke Manchester a Ingila.

A shekarar 2019 Bronze ta zama 'yar kwallon Turai da ba kamarta, sannan ta yi ta biyu a gasar Ballon d'Or wadda Rapinoe ta lashe.

Jerin matan da suka lashe kyautar gwarzuwar kwallon kafa ta BBC ta shekara

2015: Asisat Oshoala (Nigeria)

2016: Kim Little (Scotland)

2017: Ada Hegerberg (Norway)

2018: Lucy Bronze (England)

2019: Ada Hegerberg (Norway)

2020: Lucy Bronze (England)

Labarai masu alaka