An dage gasar Olympic 2020 saboda coronavirus

Olympics 2020 Hakkin mallakar hoto Getty Images

An dage wasannin Olympic da birnin Tokyo ya shirya karbar bakunci a bana, zuwa shekara mai zuwa, saboda coronavirus.

Tun farko an tsara fara gasar daga ranar 24 ga watan Yulin shekarar nan, amma yanzu za a gudanar da shi a shekara mai zuwa in ji kwamitin Olympic na duniya.

Haka kuma an dage wasannin Olympic na nakasassu zuwa 2021.

Kwamitin Olmpic ya ce za a kira gasar Tokyo 2020 duk da a shekarar 2021 ake gudanar da wasannin.

Wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin kwamitin Olympic da masu shirya gudanar da wasannin ta ce ''Daukar matakin ya zama wajibi ganin yadda annobar coronavirus ta game duniya''.

A ranar Litinin daraktan hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce annonar COVIC-19 na ci gaba da ruruwa.

Kimanin mutum 375,000 ne suka kamu da cutar a fadin duniya a kusan dukkan kasashe, ana kuma samun karin wadanda ke kamuwa da annobar a kowanne lokaci.

Ba a taba dage gasar Olympic ba a cikin shekara 124 da ake gudanar da wasannin, illa an taba soke bikin 1916 da na 1940 da kuma 1944 a lokacin yakin duniya na daya da na biyu.

Labarai masu alaka