Mai kungiyar Olympiakos ya warke daga coronavirus

Evangelos Marinakis Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mai kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest da kuma Olympiakos Evangelos Marinakis ya ce ya warke daga coronavirus.

Marinakis ya kamu da cutar ranar 10 ga watan Maris, bayan kwana hudu da ya kalli wasan Nottingham da Millwall a gasar Championship.

Ya yaba kan yadda Girka ta tanadi kayayyakin lafiya, ya kuma yi godiya ga wadanda suka yi jinyarsa har ya samu sauki.

''Bayan da na yi mako biyu ina jinya, likitoci sun sake auna ni a karo na biyu, inda suka sameni da koshin lafiya'', in ji mai shekara 52 a kafar intanet ta Forest.

Marinakis wadda ya mallaki Forest a watan Mayun 2017 ya yi kira da mutane su dauki dukkan matakan kare kansu da na iyalai daga kamuwa da annobar.

Labarai masu alaka