Bernabeu ya zama cibiyar raba magunguna don yakar coronavirus

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Filin wasa na Real Madrid, Santiago Bernabeu zai samar da wurin ajiye magunguna da aka bayar na gudunmawa don yakar coronavirus.

Hakan ya biyo bayan da kungiyar ta cimma yarjejeniya da babbar cibiyar wasanni ta Spaniya don karba da raba magunguna don yaki da cutar da ta addabi duniya.

Duk magungunan da aka samu za a bai wa hukumar lafiya ta Spaniya da amincewar gwamnatin kasar don yaki da coronavirus da ke neman tsayar da dukkan al'amura.

Haka kuma Real Madrid za ta tsara yadda za ta dunga karbar taimako daga kamfanoni da 'yan kasuwa musamman da suka shafi wasanni, wadanda ke son bayar da kudi ko kayayyaki da za a bai wa ma'aikatar lafiya.

An tsara shirin da babban jami'in hukumar lafiya da ke Valdemore zai sa ido don bayar da taimako ga wuraren da ke neman agajin gaggawa.