Real Madrid na son dauko Haaland, za a sabunta kwangilar Ighalo

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Real Madrid na sha'awar sayo matashin dan wasa Erling Braut Haaland, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund a bazara. Borussia Dortmund ta sayo dan kasar ta Norway ne a bazarar da ta wuce kuma za ta iya sallami shi a kan £50m. (Standard)

An shaida wa kungiyoyin da ke buga gasar EFL cewa ba za a koma fagen tamaula ranar 30 ga watan Afrilu ba inda ake sa ran sanar da sabuwar ranar da za a koma buga gasar makon gobe, a yayin da ake ci gaba da fama da annobar coronavirus. (Mail)

Shanghai Shenhua ta yi wa dan wasan da ta bai wa Manchester United aro Odion Ighalo, mai shekara 30, tayin tsawaita zamansa a can na shekara biyu inda za ta rika biyansa fiye da £400,000 duk mako. (Sky Sports)

Manchester United na son tsawaita kwantaragin Paul Pogba, mai shekara 27, sai dai hakan na iya "bata ran" dan wasan na kasar Faransa wanda ya taba lashe Kofin Duniya. (AS - in Spanish)

Dan wasan tsakiya na Spain Pedro, mai shekara 32, ya ce zai bar Chelsea a karshen kakar wasa ta bana idan kwangilarsa ta kare a kungiyar. (Independent via Cadena Ser)

Everton na cikin kungiyoyi hudu da suka yi tayin sayo dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel, mai shekara 23, wanda za a sayar a kan kusan £30m. (Sky Sports)

Barcelona na son dauko dan wasan da ya fi tsada a Tottenham Tanguy Ndombele, mai shekara 23, wanda ya koma Tottenham daga Lyon a bazarar da ta wuce a kan £55m. (Mundo Deportivo via Star)

Tottenham ta soma tattaunawa da dan wasan Ingila Oliver Skipp, mai shekara 19, da zummar sabunta kwangilarsa. (Football Insider)

Chelsea, Real Madrid, Barcelona da kuma Bayern Munich suna sanya ido kan matashin dan wasan Espanyol dan kasar Spain Nico Melamed, mai shekara 18, wanda za a sayar a kan £7.3m. (Gianluca Di Marzio - in Italian)

West Ham, Sporting Lisbon da kuma Anderlecht na cikin kungiyoyin da ke sanya ido kan golan Liverpool dan kasar Jamus Loris Karius, mai shekara 26, wanda Besiktas ta karbi aronsa kuma za a sayar da shi a kan £4.5m a karshen kakar wasan da muke ciki. (Voetbal24 - in Dutch)

Arsenal na sha'awar sayo dan wasan Valencia dan kasar Spain Carlos Soler, mai shekara 23, inda kungiyar ke son sayar da wasu 'yan wasanta domin cika lalitarta. (Sky Sports)

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka