Coronavirus: Mourinho ya saba dokar ba da tazara

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Tottenham, Jose Mourinho ya ce ya amince ya karya dokar bayar da tazara da gwamnati ta gindaya saboda kaucewa yada coronavirus.
An ga hoton Mourinho yana jan ragamar atisaye da dan kwallon da Tottenham ta saya mafi tsada Tanguy Ndombele ba tare da tazara ba a Hadley Common.
An kuma dauki hoton Sanchez da kuma Ryan Sessegnon suna gudu tare babu tazara a tsakaninsu a London Park.

Asalin hoton, @Mikalisyid
Shi kuwa Serge Aurier bidiyon kansa ya dauka yana atisaye da wani daf da juna ya kuma saka a shafinsa na sada zumunta na Instagram.
Mourinho ya ce laifin da ya aikata ba ya yi ne don karya ka'idar da gwamnati ta gindaya ba, amma dai ya na cudanya da wadanda suke tare a kowanne lokaci kawai.
Magajin garin Landan, Sadiq Khan ya ce kamata ya yi Mourinho da 'yan wasa su zama masu halayyar da za a koya.
An dakatar da wasannin Premier tun a cikin watan Maris saboda tsoron yada coronavirus.

Asalin hoton, @Mikalisyid