Yadda dan kwallon Najeriya, Chineme Martins ya mutu a fili

  • Daga Adebola Adebanjo da Piers Edwards
  • BBC Afirka bangaren wasanni
Chineme Martins
Bayanan hoto,

Chineme Martins mai shekara 23 ya mutu ne bayan ya fadi a fili a gasar lig ta Najeriya wata daya da ya gabata

Cikin watan Disamban 2018 a filin wasa da ke Lafiya a jihar Nasarawa aka buga wasan sada zumunta tsakanin Nasarawa United da FC Abuja.

Ana tsaka da wasan ne Dominic Dukudod ya fadi a cikin fili, an kuma yi kokarin ceto ransa amma abin ya ce tura, bayan da Dukudod wanda ake cewa yana fama da ciwon zuciya ya mutu a hanyar kai shi asibiti.

Duk da kokarin ceto ransa da aka yi a cikin filin wasa, babu wanda zai ce maka ga wata na'urar da aka yi amfani da ita wajen taimakawa zuciyar tasa ta ci gaba da buga wa.

Haka kuma Nasarawa United wadda ta ke cikin 'yan kasan teburi za ta buga wasa a gida da Katsina United ranar 8 ga watan Maris wata daya tsakani.

Dan wasan tsakiya na Nasarawa United, Chineme Martins na fatan yin bajinta a karawar - hakan ne ya sa ya dauki hoton teburin gasar Firimiyar ya aikewa dan uwansa tare da sakon cewar ''kalli matakin da muke a kasan teburi za mu kara yin sama bayan wasa da Katsina.''

A makonnin baya Nasarawa ta samu sakamako mai kyau da ya sa ta bar cikin 'yan kasan teburi, wannan karon suna bukatar cin wasan domin ci gaba da zama a gasar a badi.

A zagaye na biyu a wasan Nasarawa ta ci kwallo 3-0 nan take ta koma ta 13 a teburi da tazarar kungiyoyi hudu kan ka tarar da 'yan karshen teburi a gasar da kungiyoyi 20 ke fafatawa.

Alkalin wasa na busa usur din karshe 'yan wasa suka fadi a fili suna ta kuka, sai dai ba kukan murna ba ne illa na rashi da aka yi musu.

Tun ana minti biyu a je hutun rabin lokaci dan wasa Chineme, mai shekara 23 ya fadi a cikin fili - daga nan ya rasa ransa.

Bayanan hoto,

Michael Martins da dan uwansa marigayi Chineme

Kungiyar Nasarawa United tana da na'urar da ke taimakawa marar lafiya numfashi da zarar ya kamu da bugun zuciya tun kan mutuwar Dukudos.

Likitan Nasarawa United, Abdul Suberu ya shaida wa BBC cewar "na'urar tana nan a filin wasa, amma ba sa amfani da ita.

Rashin yin abin da ya dace

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Daya daga rashin nasara da aka yi wajen kasa duba lafiyar Chineme kamar yadda ya ya kamata da za a iya cetar ransa.

Akwai batun rashin kayan aiki da yadda ya kamata a kula da marar lafiya a matakin gaggawa zuwa asibiti da hakan ke taimakawa wajen cetar ran dan wasa.

Yawancin 'yan wasan kwallon Najeriya kusan dozin biyu na mutuwa ne ta hanyar daukewar bugun zuciya a shekara 25 da suka wuce, ko a gida ko a wasu kasashen.

Saboda haka ya zama wajibi a samar da na'urar da take taimakawa wajen farfado da masu bugun zuciya a kowanne filayen kwallon Najeriya.

Tun a 2015 hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya ta bai wa Nasarawa United na'urar.

Sai dai kungiyar ba ta gyaran na'urar duk da dokar da hukumar gasar Firimiyar ta bayar cewar a tanadi na'urar a kuma tabbatar tana aiki a lokacin da ake gudanar da gasar kasar.

Babu wani kwamishinan wasa da zai shaida wa BBC cewar an tanadi na'urar a ranar - duk da cewar kungiyoyi da hukumar kwallon kafar jiha na sa hannu kan cewar an tanadi dukkan kayan da ake bukata tun kan fara wasa.

Bayanan hoto,

Motar daukar marar lafiya a babban filin wasa da ke garin Lafiya ta kasa tashi ranar 8 Maris

Likitan kungiyar Nasarawa United ya fada cewar da 'yan wasa da likitoci da 'yan kallo duk sun garzaya don cetar rai - to amma yin hakan, karya doka ne domin cewa aka yi likitoci ko kuma kwararrun lafiya aka amince su duba dan wasa a cikin fili.

Bayan da babu na'urar da ya kamata a fili da kwarrarrun lafiya da ya kamata su duba dan wasa ga motar kai marasa lafiya asibiti taki tashi - dalilin da ya sa kenan 'yan kallo suka shiga fili, wasu ma suka taimaka wajen tura mota.

Suberu ya ce hukumar kwallon kafa ta jiha ce ke da alhakin kawo motar kai marasa lafiya asibiti a filin wasa.

Sai dai shugaban hukumar kwallon kafar jihar Nasarawa ya fadi na shi labarin na daban.

Bayanan hoto,

An diba lafiyar Chineme Martins Nasarawa United kafin soma kaka

Lokacin da Martins ke neman taimakon gaggawa yana kasa a kwance - ga babu kayayakin aikin lafiya a filin wasa sannan mota ta lalace da ya kamata ta kai shi asibiti - sai motar gwamnan jihar Nasarawa wanda ya je kallon wasan aka yi amfani da ita zuwa asibiti.

Sai dai kuma an samu rahoton da kungiyar ta ce Chineme ya mutu ne a asibiti, yayin da wani da ya ga abin da ya faru da idonsa ya ce tun a fili dan kwallon ya cika.

Ranar Laraba aka cika wata daya da Chineme ya mutu - bayan da ake ta jiran hukumar kwallon kafar kasar NFF ta fitar da dalilin da ya sa dan wasan ya mutu da hanyoyin da ya kamata a bi nan gaba don kiyaye faruwar hakan.

Bayan da dan kwallon ya mutu NFF ta sanar da dokar cewar ba za a fara wasa ba har sai an tanadi dukkan kayayyakin duba marar lafiya da taimakon gaggawa da ma'aikatan lafiya, sai kwamishinan wasa da hukumar kwallon kafar jiha sun tabbatar komai na aiki kan a fara wasa.

An ci tarar Nasarawa United sama da dala 15,000 - bayan da ta karya dokoki da dama, tun daga gazawa wajen samar da kayayyakin aiki da ma'aikatan lafiya da suka kamata a lokacin, da kuma barin mutane da dama suka shiga fili a lokacin cetar rai da amfani da motar daukar marasa lafiya wadda ta kasance a lalace.

A wasa na gaba da Nasarawa United za ta buga sai ga shi ta tanadi motar kai marasa lafiya asibiti ba guda daya ba har uku a cikin fili.

Bayanan hoto,

Motocin daukar marar lafiya uku aka gani bayan dan wasa ya mutu a fili