Sancho ba ya son komawa Chelsea, Barcelona na zawarcin Ndombele

Jadon Sancho

Asalin hoton, PA Media

Dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, ba ya sha'awar komawa Chelsea, lamarin da ya bai wa Manchester United damar zawarcinsa, ko da yake har yanzu Real Madrid na da damar dauko shi. (Diario Madridista, in Spanish)

Barcelona ce a kan gaba wajen zawarcin dan wasan Tottenham dan kasar Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 23(Star)

Everton ta bi sahun wasu kungiyoyi da ke son dauko dan wasan Real Madrid dan kasar Colombia James Rodriguez. Manchester United da Juventus na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan mai shekara 28. (Express)

Chelsea za ta sake taya dan wasan Napoli da Belgium Dries Mertens. A watan Janairu kungiyar ta soma taya dan wasan mai shekara 32 ko da yake an ki amincewa da tayin nata, amma har yanzu Mertens bai sanya hannu kan sabon kwantaragi a Napoli ba. (Gazetto dello Sport, in Italian)

Roma na jan kafa wajen biyan Arsenal £22m don dauko dan wasanta na tsakiya Henrikh Mkhitaryan. Dan wasan dan kasar Armenia mai shekara 31, yana can kungiyar da ke buga gasar Serie A a matsayin aro. (Calciomercato, via Star)

Mai yiwuwa dan wasan Inter Milan Lautaro Martinez, mai shekara 22, ya bi sahun dan kasarsa ta Argentina Lionel Messi wajen komawa Barcelona, a cewar wakilinsa. A baya an yi hasashen cewa dan wasan mai shekara zai koma Manchester City. (Fox Sports Mexico, in Spanish)

A wani gefen, mataimakin shugaban Inter Milan Javier Zanetti ya yi amannar cewa Martinez zai ci gaba da zama a kungiyar. (ESPN)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A wani labarin kuma, mai yiwuwa dan wasan Inter Milan da Uruguay Diego Godin ya koma wata kungiya da ke buga Gasar Firimiya. Manchester United da Tottenham na son dauko dan wasan mai shekara 34. (Tuttosport, in Italian)

Shugaban Tottenham Daniel Levy zai iya hana duk wani yunkuri na dauko dan wasan Chelsea da Brazil Willian, a cewar tsohon dan wasan Ingila Danny Mills. A baya dan wasan mai shekara 31 ya ki karbar tayin komawa Tottenham duk da cewa an kammala yi masa gwajin lafiya a 2013. (Football Insider)

Kocin Southampton Ralph Hasenhuttl ya amince ya sanya hannu kan sabon kwantaragi na shekara uku a kungiyar. (Sun)

Arsenal na kokarin yin tsimin £25m ta hanyar rage albashin 'yan wasanta idan basu cancanci zuwa Gasar Zakarun Turai ba. (Telegraph, subscription required)

Dan wasan West Ham da Ingila Declan Rice ya ce yana son sake buga tamaula tare da dan wasan Chelsea Mason Mount . 'Yan wasan biyu, masu shekara 21, sun taba yin wasa tare a makarantar koyar da 'yan kwallon kafa ta Chelsea. (Copa90)

Dan wasan Ingila Phil Jones, mai shekara 28, ya ce ya ki karbar tayin komawa Manchester City, Liverpool da kuma Arsenal kafin ya koma Manchester United a 2011. (MUTV)