Coronavirus: Kungiyoyin Premier za su yi taro kan yadda za a karkare gasar bana 30 ga Yuni

  • By Simon Stone
  • BBC Sport
Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyoyin Premier League za su tattauna kan yadda za a karkare wasannin kakar bana

Ranar Juma'a kungiyoyin da ke buga gasar Premier League za su tattauna kan batun karkare kakar 2019/20 ranar 30 ga watan Yuni.

Ba dukkan kungiyoyin za a gayyata taron da za a gudanar kan yadda za a karkare wasannin bana ba, inda ake sa ran ci gaba da wasannin cikin watan Mayu, bayan da kulub -kulob ke tunanin yadda yadda za su sha kan 'yan wasa da yarjejeniyarsu za ta kare a bana.

'Yan wasa da dama ne kwantiraginsu zai kare da kungiyoyinsu ranar 30 ga watan Yuni, wasu daga cikinsu har da Willian na Chelsea da dan kwallon Tottenham Jan Vertongen.

Lokaci ya yi da kungiyar Liverpool ya kamata ta sake kamfanin da zai dauki nauyin rigar da za su saka daga New Balance zuwa Nike, ita ma Watford da Newcastle za su sake kulla yarjejeniya da wasu kamfanunuka.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta kwan da sanin wadan nan matsalolin tana kuma shirin zakulo hanyoyin da ya kamata a warware wannan sarkakiyar sakamakon cutar korona.

Haka kuma a doka ba za a tursasa wa 'yan wasa sai sun sa hannu kan yarjejeniya ba, hakan kuma zai iya sa kungiya ta yi hasarar fitattun 'yan wasanta tun kan a kammala wasannin bana.

Hakan ne ya sa wasu da dama ke bayyana ra'ayinsu cewar ya zama wajibi a karkare gasar Premier League ranar 30 ga watan Yuni.

Sai dai kuma a kwai matsala da zarar an karkare lokacin karkare wasannin bana, musamman batun kungiyoyin da za su fado daga Premier da wadanda za su maye gurbinsu.

Wasu sun bayar da sharawar cewar kungiyar da ke kan gaba a gasar Championship wato Leeds United da West Brom su haura gasar Premier, ita kuma babu wadanda za a zubar, sai kungiyoyi 22 su fafata a kakar badi ta 2020/21.

Sai dai kuma hakan zai kawo rashin daidaituwar kungiyoyin da ya kamata su buga kananan rukunoni na gasar Ingila wato Football Legue.

A kwai dai batutuwa da dama da za a tattauna ranar Juma'a kan yadda ya kamata a karkare wasannin Premier bana, bayan da hukumar kwallon kafar Turai ke fatan mambobinta su samar da matsaya kan yadda kowacce kasa za ta rufe wasannin shekarar nan.