Coronavirus: 'Yan wasan Arsenal da koci sun rage kaso 12.5 na albashinsu

Arsenal players celebrate a goal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a biya 'yan wasa da koci kudin da suka rage idan sun kai kungiyar wasan zakarun Turai na Champions League ko na Europa League

'Yan kwallon Arsenal da koci Mikel Arteta sun rage kaso 12.5 cikin 100 na albashi saboda halin da cutar korona ta haddasa.

Kungiyoyin Premier sun ce wannan yarjejeniya ce don radin kai wadda ta hada da yanke kaso 12.5 da kudin da mutun ke dauka a duk shekara.

Sauran masu horas da 'yan wasa suna da cikin wadanda suka amince a rage musu alabashin.

Arsenal ta ce idan kungiyar ta taka rawar gani a sauran wasannin da suka rage mata, to za ta biya kason da ;yan wasa da koci suka amince.

Cikin fatan da Gunners ke yi ya hada da samun gurbin shiga gasar Zakaraun Turai ta Champions League ta kakar badi wato 2021-22 kamar yadda BBC ta bayar da rahohon fatan Arsenal a makon jiya.

'Yan kwallon za su samu ladan fam 100,000 idan suka kai gasar Champions League ta badi, Sannan kowanne dan kwallo zai samu fam 500,000 idan Arsenal ta lashe kofin Zakaraun Turai, ko kuma fam 100,000 idan suka lashe Europa League na badi.

Arsenal ta ce ''Za mu biya kudin da 'yan wasa da koci suka rage da zarar sun kai mu gasar Zakarrun Turai ta Champions League ko Europa ta bana, don za mu samu kudin da za mu yi dawainiya.''