Coronavirus: Masu daukar nauyi za su yi amfani da Nou Camp don tara kudi

Nou Camp

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona ta fara wasa a Nou Camp tun 1957

Barcelona za ta bai wa masu daukar nauyinta damar amfani da filin Nou Camp a karon farko don tara kudin da za a yaki cutar korona.

Ba a taba sauya sunan filin Barcelona da ake kira Nou Camp da ke birnin Catalan ba tun lokacin da aka bude a 1957.

Mai rike da kofin La Liga ta bai wa gidauniyar Barcelona damar samum wadanda za su dauki nauyin kakar 2020-21.

Kungiyar ta ce kudin da za a samu za ta yi amfani da shi ne wajen binciken maganin cutar korona.

Spaniya daya ce daga kasashe hudu da mutun sama da 20,000 cutar corona ta hallaka.

A shekarar 2010 Barcelona ta kulla yarjejeniya da gidauniyar Qatar domin daukar nauyinta, koda yake tana sa bajon tallafin Unicef a rigarta tun daga 2006.