Uefa na diba yiyuwar soke wasu wasannin Turai

Uefa Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu ba a kammala wasannin zagaye na biyu a Champions League ba

Uefa ta bayar da shawarar cewar sai dai a soke wasu gasar kwallon kafa ta bana, sakamakon tsaiko da cutar korona ta haddasa.

A ranar Talata mambobin hukumar kwallon kafar Turai su 55 suka tattauna ta bidiyo domin zakulo hanyar da za a karkare wasannin bana.

Sun kuma amince da a koma wasanni a watan Yuni, sannan a karkare gasar Champions League ranar 29 ga watan Agusta.

Tun farko Uefa ta ja kunne cewar duk wadanda suka kammala gasar kasarsu a wannan yanayin za su iya rasa gurbin Champions League da Europa League.

Rashin tabbas kan lokacin da ya kamata a karkare wasannin bana kan yadda cutar korona ke kashe mutane ya sa a karon farko Uefa ta yadda cewar wasu mambobinta ba za su iya kammala wasanninsu na bana ba.

An kuma bayar da shawarar kan yadda wasu kasashe ya kamata su karkare wasanninsu, an kuma sanar da Uefa kan matakan da ya kamata ta bi ga wadanda ba su kammala gasar ba - da ya kamata su samu gurbin Champions League da Europa League.