Chelsea za ta dauko Aubameyang da Osimhen, Barcelona na zawarcin Ndombele

Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea tana sanya ido kan halin da Pierre-Emerick Aubameyang yake ciki a Arsenal inda take fatan dauko dan wasan na Gabon a bazara. (ESPN)

Kazalika Chelsea ta amince ta kara shekara daya a kwangilar dan wasan Faransa, Olivier Giroud, mai shekara 33. (Di Marzio - in Italian)

Sannan kungiyar ta Chelsea ta tuntubi Lille domin dauko dan wasan Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 21. (Le10Sport - in French)

Barcelona tana son sayo dan wasan Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 23, daga Tottenham kuma ta amice da wata yarjejeniya da za ta kai ga mika wa Tottenham 'yan wasa biyu, wato Samuel Umtiti, mai shekara 26, da Nelson Semedo. (Sky Sports)

Chelsea tana ci gaba da rike golan Spaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, duk da sha'awar da take yi ta sayo dan wasan AC Milan dan kasar Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 21. (Mail)

Daraktan wasanni na RB Leipzig Markus Krosche ya ce ba a tuntube su kan dan wasan Jamus Timo Werner ba a makonnin baya baya nan duk da rade radin da ake yi cewa Liverpool da Barcelona suna zawarcin dan wasan mai shekara 24. (Goal)

Manchester City, Paris Saint-Germain da kuma Juventus suna zawarcin dan wasan Lyon Houssem Aouar, mai shekara 21. (RMC Sport - in French)

Mamallakin Napoli Aurelio De Laurentiis ya bayyana farashin da ya sanya kan dan wasan kungiyar Fabian Ruiz, mai shekara 24, a yayin da Manchester City take son sayo dan wasan. (Teamtalk)

Everton ta tuntubi Barcelona kan yiwuwar dauko dan wasan Brazil Emerson, wanda yanzu haka yake zaman aro a Real Betis. (Sport - in Spanish)

Real Betis tana son karbo aron dan wasan wasan Barca dan kasar Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27. (Sport - in Spanish)

Roma tana shirin bai wa dan wasan Napoli da Belgium Dries Mertens kwangilar shekara uku. (Corriere dello Sport, via Goal in Italian)

Aston Villa da Crystal Palace suna son dauko tsohon dan wasan Liverpool Fabio Borini. Dan wasan na Italiya mai shekara 29 yanzu haka yana murza leda a Hellas Verona. (L'Arena - via Birmingham Mail)