Raheem Sterling ya ce yana son rigar wasan Lionel Messi

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Raheem Sterling ya ce Ronaldinho ne ya sanya masa sha'awar tamaula

Dan wasan Manchester City Raheem Sterling ya lashe kofuna da dama, ya zura kwallo fiye da 100 a tarihinsa na kwallon kafa sannan ya samu lambar yabo 56 a Ingila, amma duk da haka burinsa ba zai cika ba sai ya samu abu daya - jesi ko kuma rigar wasan Lionel Messi.

Duk da yake ya karbi rigunan wasan 'yan kwallon kafa da dama, sai dai har yanzu bai karbi rigar shahararren dan wasan Barcelona ba.

“Akwai abu daya kacal da nake matukar so kuma wannan abu shi ne rigar wasan Messi,” in ji Sterling.

"Lokacin da muka yi wasa da Barcelona, na karbi rigar Neymar. Ita ce jesi ta farko da na soma tambaya a ba ni.

"Ina fatan zan samu rigunan wasa da dama kafin na kammala sana'ar kwallon kafa na zauna wuri daya, inda zan zabi wadanda suka fi burge ni, sannan na samu dakin ajiye kofunan da na lashe da kuma rigunan wasan da aka ba ni.”

Ko da yake rigar wasan Messi ce ta farko a cikin jerin abubuwan da yake so, amma Sterling ya ce ba Messi ne dan wasan Barcelona da ya karfafa masa gwiwar soma buga tamaula ba.

Sterling ya shaida wa BBC Sport cewa "Ronaldinho ne dan wasan da ya sanya min sha'awar kwallon kafa. Idan ka duba adadin bidiyon da na kalla a Youtube, za ka ga cewa na kalli dukkan bidiyonsa na sana'ar kwallon kafa.

“Na sha zuwa lambu inda nake kokarin kwatanta yadda yake murza leda, ko da yake ban iya ba. Na yi bakin kokarina. Shi dan wasa ne na musamman.”