'Yan wasan FC Cologne uku sun kamu da cutar korona

FC Cologne

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sauran 'yan wasan FC Cologne na cikin fargaba

'Yan wasan kungiyar FC Cologne ta kasar Jamus guda uku sun harbu da cutatr korona, kamar yadda kulob din ya tabbatar.

Kungiyar ta Bundeliga ta ce an yi wa baki dayan tawagar gwajin korona a ranar Alhamis.

Mutum ukun da suka kamun ba su nuna alamun cutar ba tukunna, a cewar kungiyar, amma za su shafe kwana 14 a killace a gidajensu. ta ce za a ci gaba da atsaye a kungiyar.

Kulob din bai bayyana wadanda suka harbu da cutar da ake yi wa lakabi da Covid-19 ba.