Hertha ta dakatar da Kalou, bayan karya dokar hana yada cutar korona

Hertha Berlin Solomon Kalou

Asalin hoton, Getty Images

Hertha Berling ta dakatar da Solomom Kalou, bayan da ya sa bidiyonsa a Facebook ya mika wa abokin wasansa hannu suka gaisa da kuma yin cudanya da mutane.

Hakan ya karya dokar da gwamnatin Jamus ta kafa ta bayar da tazara idan za a yi hulda, duk don hana yada cutar korona.

Kungiyar ta ce wannan laifi ne da dan kwallonta daya tal ya aikata, ta kuma musanta batun cewar 'yan wasanta ba sa daukar tsafta da bayar da tazara da muhimmaci.

Dan wasan tawagar Ivory Coast ya nemi afuwa, sai dai mahukuntan gasar Jamus sun kwatanta lamarin da ba za su amince da shi ba.

Wasu kafafen yada labarai a kasar na cewar abin da Kalou ya yi zai iya kawo koma baya a shirin da ake yi na ci gaba da gasar Bundesliga ta 2019-20.

A cikin watan Maris aka dakatar da wasannin tamaula a Jamus don gudun yada cutar korona, amma yanzu ana sa ran gwamnati za ta amince a karkare kakar bana cikin makonni masu zuwa.

Hertha ta ce Kalou ya yi bidiyon ne, bayan da aka gwada dukkan 'yan wasan kungiyar kuma babu mai dauke da annobar.

Tsohon dan wasan Chelsea da Lille da Feyenoord wanda ya yi wa tawagar Ivory Coast wasa 90 ya nemi afuwa ya kuma nemi gafara ga mutanen da ya yi bidiyon ba tare da sun sani ba.