Coronavirus: 'Yan wasa 10 da ke gasar Jamus sun kamu da cutar korona

Schalke in training

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyoyi a Jamus na atisaye amma suna bayar da tazara tsakanin 'yan wasa

An samu 'yan kwallo 10 dauke da cutar korona daga manyan kungiyoyi biyu da ke buga gasar Jamus, bayan gwada mutum 1,724 da aka yi.

Mahukuntan gasar Jamus ne suka tabbatar da hakan, koda yake tuni wasu kungiyoyin da ke buga gasar kasar suka fara atisaye cikin rukuni a shirin da ake yi na karkare kakar 2019-20.

Mahukuntan sun ce tuni aka dauki matakan killace 'yan kwallon da aka samu dauke da annobar.

Kawo yanzu FC Cologne ba ta da wani dan kwallo da ke dauke da cutar, bayan da aka samu 'yan wasa uku a makon jiya da cutar korona.

An kuma killace 'yan wasa wadanda yanzu ba su da alamar cutar, amma za su yi kwana 14 kafin su koma mu'amala da sauran 'yan kwallon Cologne din.

A cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin tamaula a Jamus, bayan da cutar korona ta bulla.

Jamus za ta zama ta farko a Turai da za ta koma ci gaba da gasar kwallon kafa don karkare kakar 2019-20.