Bayern Munich ta nada Klose a matsayin mataimakin koci

Miroslav Klose

Asalin hoton, Getty Images

Bayern Munich ta nada Miroslav Klose a matsayin mataimakin koci kan kwantiragin kaka daya.

Klose, wanda ya ci kwallo 16 ya kuma lashe kofin a gasar cin kofin duniya a 2014 yana aiki da Bayern a matakin kocin 'yan kasa da shekara 17 kan yaejejeniyar shekara biyu tun daga 2016.

A ranar 1 ga watan Nuwambar 2016 aka dauki Klose aka bai wa aiki cikin masu horas da tawagar kwallon kafar Jamus.

Klose zai yi aiki a matakin mataimakin Hansi Flick a Bayern Munich daga farkon kakar badi.

Dan wasan Jamus, ya taka leda a Kaiserslautern da Werder Bremen da Bayern Munich da kuma Lazio ta Italiya.