Coronavirus: Za a ci gaba da Bundesliga ba 'yan kallo daga 16 ga Mayu

Asalin hoton, Getty Images
Za a ci gaba da gasar Jamus ta Bundesliga ranar Asabar 16 ga watan Mayu ba tare da 'yan kallo ba, domin a karkare kakar 2019-20.
Hakan zai sa gasar za ta zama ta farko a nahiyar Turai da za a ci gaba da buga kwallon kafa, tun bayan da cutar korona ta haddasa tsaiko.
Cikin wasannin farko da za a yi ranar Asabar har da na hamayya tsakanin Schalke da Borussia Dortmund.
Mai rike da kofin bara, Bayern Munich, wadda ke mataki na daya a kan teburin bana da tazarar maki hudu za ta ziyarci Berling ranar Lahadi.
Sauran wasa 11 a kammala kakar shekarar nan, kuma tsakanin 27 zuwa 28 ake sa ran buga wasannin makon karshe a gasar ta Bundesliga ta bana.
Hukumar kwallon kafar Jamus ta ce za a koma wasannin ne. bayan da aka cimma yarjejeniyar kula da lafiya, kuma babu 'yan kallo, sannan za a yi wa 'yan kwallo gwajin cutar korona.
Mutum 300 da ya hada da 'yan wasa da jami'ai da ma'aikata aka sa ran su kasance a cikin fili a lokacin da ake gudanar da wasannin.
Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa a Jamus don gudun yada cutar korona, yayin da 'yan wasa suka koma yin atisaye a tsakiyar Afirilu tare da matakan hana yada annobar.
Ga jadawalin wasannin da za a buga
Ranar Asabar
- Augsburg da Wolfsburg
- Borussia Dortmund da Schalke
- Eintracht Frankfurt da Borussia Monchengladbach
- Fortuna Dusseldorf da Paderborn
- Hoffenheim da Hertha Berlin
- RB Leipzig da Freiburg
Ranar Lahadi
- Cologne da Mainz
- Union Berlin da Bayern Munich
Monday
- Werder Bremen da Bayer Leverkusen