United za ta maye gurbin De Gea, Tottenham za ta dauko Meunier

David de gea

Asalin hoton, Getty Images

Jaridar Sun ta rawaito cewa Tottenham tana gaban Manchester United a kokarin da suke yi na sayo dan wasan Paris St-Germain dan kasar Belgium Thomas Meunier, mai shekara 28.

Manchester United tana duba yiwuwar maye gurbin David de Gea, duk da yake golan na kasar Spaniya mai shekara 29 ya sabunta kwangilarsa zuwa shekara hudu a kungiyar, in ji Mirror.

Manchester United tana shirin dauko dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, amma Barcelona da PSG suna zawarcin dan wasan mai shekara 22. (Express)

Kazalika Manchester United, Chelsea da kuma Tottenham suna sha'awar sayo dan wasan Lazio dan kasar Serbia Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 25. (Caught Offside)

Liverpool ta shirya dauko dan wasan Brazil mai shekara 17, Talles Magno, wanda yake murza leda a kungiyar Vasco de Gama da ke Rio de Janeiro.(Star)

Hakazalika Liverpool za ta iya dauko dan wasan baya na Arsenal Bukayo Saka, a yayin da tattaunawar da ake yi kan kwangilar dan kwallon kafar mai shekara 18 ta cije. (Sun)

Tsohon dan wasan Tottenham Darren Bent ya yi kira ga kungiyar da ta sayo dan wasan Bournemouth dan kasar Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, a bazara.(Express)

Dan wasan Real Madrid mai shekara 23 dan kasar Spaniya, Dani Ceballos, wanda yake zaman aro a Arsenal, ya yi amfani da wani hoton barkwanci na Donald Trump wajen musanta rade radin da ake yi cewa zai koma Sevilla(Sun)

Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce a ko yaushe za a rika daukar Liverpool a matsayin kungiyar da ta lashe Gasar Firimiya ta bana, ko da kuwa an soke kakar wasa ta bana. (TalkSport via Express)