Coronavirus: An samu 'yan wasa biyar da cutar korona a Spaniya

Asalin hoton, Reuters
A karon farko Lionel Messi ya yi atisaye a Barcelona ranar Juma'a tun bayan ata biyu
'Yan wasa biyar masu buga gasar Spaniya babba da karama na dauke da cutar korona in ji mahukunta wasannin.
Kawo yanzu ba a bayyana sunan 'yan kwallon da suka kamu da annobar ba, sai dai an killace su.
Za kuma a ci gaba da gwada su, kuma har sai sun warke kafin su koma atisaye cikin sauran 'yan wasa.
A makon jiya mahukuntan La Liga suka fara auna lafiyar 'yan kwallo da nufin shirye-shiryen fara atisaye don karkare kakar 2019-20.
Mahukuntan gasar La Liga na fatan ci gaba da gasar shekarar nan ba tare da 'yan kallo ba a cikin watan Yuni.
A makon jiya ne wasu kungiyoyin Spaniya suka fara atisaye ciki har da Barcelona.
Spaniya daya ce daga kasashen da cutar korona ta kassara a Turai, inda mutum 224,390 suka kamu da annobar sannan ta hallaka 26,621 kawo zuwa 10 ga watan Mayu.