Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Bale, Ndombele, Sancho, Ighalo, Pogba, Messi

Gareth Bale

Asalin hoton, Getty Images

Newcastle ta shirya kashe £53m don sayo ɗan wasan gaban Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 30, a cewar (Daily Mail).

Tottenham ba za ta bar ɗan wasan da ta sayo a kan £55m Tanguy Ndombele, mai shekara 23, ya bar kungiyar a bazara ba. Ana hasashen cewa ɗan wasan na Faransa zai koma Barcelona ko Liverpool. (Independent)

Da alama Dejan Lovren yana haɗa jakarsa domin barin Liverpool, inda ake rade radin Roma za ta ɗauko dan wasan na kasar Croatia mai shekara 30. (Gazzetta dello Sport, via Liverpool Echo)

Liverpool ta bi sahun manyan kungiyoyin Turai a zawarcin dan wasan Red Bull Salzburg ɗan kasar Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekara 19. (Tuttosport, via Daily Mail)

Manchester United tana son dauko 'yan wasa uku a bazara - ɗan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 20, ɗan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, da kuma ɗan wasan Birmingham Jude Bellingham, mai shekara 19. (Daily Star)

Sai dai watakila wannan ne karon karshe da dan wasan Najeriya, Odion Ighalo, mai shekara 30, zai buga wasa a Manchester United bayan tattaunawar da take yi da Shanghai Shenhua ta China ta ci tura. (Standard)

Juventus ta zama kungiyar kwallon kafar Italiya ta farko da za ta kaddamar da shirin kayyade yawan albashi, abin da ke nufin ba za su iya sayen dan wasan Manchester United mai shekara 27 dan kasar Faransa Paul Pogba ba. (Daily Mail)

Lionel Messi, mai shekara 32, da sauran 'yan wasan Spaniya suna fuskantar yiwuwar rage albashinsu da kashi 30 cikin 100 a kakar wasa mai zuwa a yayin da Barcelona da Real Madrid suke fama da karancin kudin shiga sakamakon annobar korona. (Sun)

Chelsea tana da kwarin gwiwar dauko dan wasan Manchester United mai shekara 19 Angel Gomes. (Mirror)

West Brom za ta fafata da Tottenham a yunkurin sayo dan wasan Fenerbahce da Kosovo Vedat Muriqi, mai shekara 26, wanda za a sayar a kan £18m idan suka masu matsayin buga gasar Premier. (Aksam, via Birmingham Mail)

Crystal Palace tana son dauko kocin Burnley Sean Dyche don zaman sabon kocinta. (Mirror)