Muna shan kakkausar suka - Kane

Harry Kane has scored 11 Premier League goals during the 2019-20 season

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Harry Kane ya zura kwallo 11 a kakar wasa ta bana a gasar firimiya

Kyaftin din Ingila, Harry Kane ya ce 'yan wasan gasar firimiyar Ingila na fuskantar suka babu gaira babu dalili a wannan lokacin na annobar korona.

Ko a watan da ya wuce, Sakataren lafiyar Biritaniya Matt Hancock ya ce kamata ya yi a rage albashin 'yan wasa.

"Muna nuna cewa muna iyaka kokarin don taimakawa ma'aikatan lafiya a wannan lokacin na annoba," in ji Kane.

Amma "muna shan suka wanda hakan babu adalci a cikinsa."

Kane ya kara da cewa ya tuntubi abokin wasansa, Dele Alli domin ya jajanta masa saboda barayi sun shiga gidansa a ranar Laraba suka yi masa sata tare da raunata shi.