Giroud zai ci gaba da taka leda a Chelsea zuwa karshen kakar badi

Olivier Giroud

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Olivier Giroud ya koma taka leda a Chelsea daga Arsenal a shekarar 2018

Dan wasan Chelsea da tawagar kwallon kafar Faransa, Olivier Giroud ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar badi.

Giroud ya buga wasan Premier League biyar a watan Janairu, yana kuma wata shida da suka rage kwantiraginsa ya kare a Chelsea.

Sai dai bayan da Tammy Abraham ya yi rauni ne kocin Chelsea, Frank Lampard ya ke amfani da Giroud, wanda ya ci kwallo biyu a wasa hudu a Premier.

Giroud mai shekara 33, ya koma Chelsea a Janairun 2018, ya buga mata wasa 39 da 37 da ya yi canji ya kuma ci kwallo 21 kawo yanzu.

Dan wasan tawagar Faransa shi ne ya ci wa Chelsea kwallo na karshe a wasan da suka doke Everton 4-0 ranar 6 ga watan Maris daga nan aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.