Coronavirus: Hukumar kwallon Italiya ta tsayar da ranar karkare Serie A ta bana

Juventus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Juventus ce kan gaba a teburin Serie A da tazarar maki daya jal

Hukumar kwallon kafar Italiya ta tsayar da ranar 1 ga watan Satumba don ci gaba da gasar Serie A ta bana, sannan a karkare kakar 2019-20 ranar 20 ga watan Agusta.

Cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni a kasar, saboda bullar cutar korona, amma yanzu hukumar na fatan karkare gasar mai mataki uku, wato Serie A da B da kuma C.

Sauran wasanni 12 suka rage wa kungiyoyin a kammala Serie A ta kakar shekarar nan da kwantan wasa hudu kawo yanzu.

Juventus wadda ke fatan lashi kofi na tara a jere tana mataki na daya a kan teburi da tazarar maki daya tal.

Hukumar ta ce koda an ci gaba da wasanni a matakan gasar uku aka kuma ci karo da tsaiko, za ta yi amfani da wasannin cike gurbi don fitar da wadanda za su wakilce ta a gasar Turai da wadanda za su fadi daga gasar bana.

Gasar Serie C ce ake da kalubale wadda ke dauke da kungiyoyi 60 da aka raba su zuwa yanki uku na kasar, wadanda da damansu ke fama da rashin kudi kawo wannan lokacin.