Mario Gotze zai bar Borussia Dortmund idan an kammala kakar 2019-20

Mario Gotze

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasa biyar Mario Gotze ya buga wa Borussia Dortmund a kakar bana

Mario Gotze zai bar Borussia Dortmund da an kammala kakar bana in ji daraktan wasannin kungiyar Michael Zorc.

Mai shekara 27 ya buga wasa 201 a kaka biyu da ya yi a kungiyar, sai dai kuma karawa biyar ya yi wa Dortmund a kakar shekarar nan.

Gotze ya lashe kofin Bundesliga biyar, kuma shi ne ya ci wa Jamus kwallo a wasan karshe da ta lashe kofin duniya a 2014.

An yanke wannan shawarar, bayan da kocin Dortmund, Lucien Favre ya ce ba shi da inda zai saka dan kwallon a lokacin wasa.

Gotze ya fara da zaman benci a karawar da Dortmund ta doke Wolfsburg 2-0 a wasan mako na 27 ba tare da 'yan kallo ba.