Za a ci gaba da gasar La Liga ranar 8 ga watan Yuni

Lionel Messi takes part in Barcelona training

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

L

Firai Ministan Spaniya, Pedro Sanchez ya ce za a ci gaba da gasar La Liga ta bana ranar 8 ga watan Yuni, amma ba 'yan kallo.

Shugaban gudanar da gasar, Javier Tebas ya ce yana fatan za a ci gaba da La Ligar shekarar nan ranar 12 ga watan Yuni, amma har yanzu ba a bayar da tabbacin ranar ci gaba da gasar ba.

A farkon makon nan 'yan wasan da ke buga gasar Spaniya suka fara atisaye amma cikin rukuni dauke da mutun 10 da kuma bayar da tazara kamar yadda gwamnati ta umarta.

A ranan ta 8 ga watan Yuni ake sa ran ci gaba da karamar gasar La Liga, kuma a babbar gasar ana sa ran buga karawar farko da wasan hamayya tsakanin Seville da Real Betis.

Ranar 12 ga watan Maris aka dakatar da gasar Spaniya don gudun yada cutar korona.

An samu 'yan wasa biyar dauke da cutar korona a La Liga da gasa mai biye da ita, nan take suka killace kansu tun daga ranar 18 ga watan Mayu.

Saura wasa 11 a kammala gasar shekarar nan, kuma Barcelona ce ta daya a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.