Liverpool tana son ɗauko Traore, Ighalo ya roƙi a bar shi ya ci gaba da zama a Man Utd

Adama Traore

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Adama Traore

Liverpool tana son dauko dan wasan Wolves dan kasar Spaniya Adama Traore, mai shekara 24, inda rahotanni suka ce kocinta Jurgen Klopp ne da kansa ya tuntubi dan wasan. (TodoFichajes - in Spanish)

Dan wasan Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, shi da kansa ya bukaci a tsawaita zaman aron da yake yia Manchester United daga kungiyar Shanghai Shenhuata kasar China. (Manchester Evening News)

Mai yiwuwa takaitaccen zaman da David Luiz yake yi a Arsenal ya zo karshe yayin da kwangilar dan wasan na Brazil mai shekara 33 za ta kare a watan gobe kuma ba a cimma wata matsaya kan sabunta zamansa ba. (Sky Sports)

Liverpool ba za ta biya £50m don sayo dan wasan RB Leipzig da Jamus Timo Werner, mai shekara 24 ba, inda ta taya shi a kan £30m a kasuwar musayar 'yan kwallon kafa. (Mirror)

Watakila dan wasanAjax da Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, ya koma Chelsea a kan £22.4m. (Telegraph - subscription required)

Tottenham tana gogayya da abokan hamayyarta na Gasar Premier a yunkurin dauko dan wasan Bournemouth da Scotland Ryan Fraser, dan shekara 26. (Football Insider)

Dan wasan Newcastle dan kasar Spaniya Javier Manquillo, mai shekara 26, yana son ya koma kasarsa don shiga kungiyar da ke buga Gasar La Liga idan kwangilarsa ta kare a watan gobe. (Newcastle Chronicle)

Manchester United da Real Madrid suna son dauko dan wasan Rennes dan kasar Faransa mai buga Gasar 'yan kasa da shekara 21, Eduardo Camavinga, dan shekara 17. (Metro)

KocinTottenham Jose Mourinho ya ce kungiyoyin da ke buga Gasar Premier ba za su "kashe mahaukatan kudade" a lokacin musayar 'yan kwallo da ke tafe ba. (Sky Sports)

An shaida wa koci-koci na kungiyoyin da ke Gasar Premier cewa za a kammala kakar wasa ta bana cikin mako shida idan shirin da ake yi a komawa Gasar ya tafi yadda ake so (Times - subscription required)