Bayern Munich za ta ɗauko Sane da Havertz, Chelsea tana kan gaba wajen zawarcin Alex Telles

Leroy Sane and Kai Havertz

Asalin hoton, Getty Images

Bayern Munich tana son dauko dan wasan Manchester City da Jamus Leroy Sane, mai shekara 24, da Kai Havertz, mai shekara 20, daga Bayer Leverkusen a wani bangare na "kawo sauyi" a kungiyar, a cewar mataimakin shugabanta. (Bayern 1, via Evening Standard)

Chelsea tana gabanParis St-Germain a yunkurin dauko dan wasan Porto dan kasar Brazil Alex Telles, mai shekara 27. (Tuttosport via Express)

Kungiyoyi da dama sun tuntubi Lille domin dauko Victor Osimhen. Tottenham, Liverpool da Arsenal suna cikin kungiyoyin da ke son dauko dan wasan na Najeriya, mai shekara 21. (Mail)

Dan wasanRB Leipzig wanda Liverpool take son daukowa Tino Werner ya yi cikakken bayani kan makomarsa idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa, a cewar daraktan wasanni na Inter Milan Piero Ausilio. Ausiollo ya ce dan wasan na Jamus mai shekara 24 "ba zai komo wurinmu ba". (Daily Star)

Arsenal ce kan gaba a kungiyoyin da ake gani za a bari su dauko dan wasan Napoli Arkadiusz Milik, mai shekara 26, ko da yake tana fuskantar gogayya daga Juventus.(La Repubblica via Daily Star)

Manchester United ta yi amannar cewa Mino Raiola, wakilin Paul Pogba, shi ne kadai mutumin da yake son dan wasan ya bar Old Trafford a bazara. Ana rade radin dan wasan na Faransa mai shekara 27 zai koma Real Madrid ko Juventus.(Times - subscription required)

Rennes ta ce ba za ta sayar da dan wasan da Liverpool da Real Madrid suke zawarci Eduardo Camavinga a azara ba. Ana rade radin cewa baya ga kungiyoyin biyu, dan wasa, mai shekara 17, zai koma Manchester United. (RTL via Evening Standard)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Dan wasanLiverpool Harvey Elliott ya yi watsi da damar da ya samu ta komawa Real Madrid. An gayyaci dan kasar ta Ingila, mai shekara 17, domin ya gana da Sergio Ramos da zummar rarrashinsa ya koma kungiyar. (The Athletic - subscription required)

Barcelona za ta bukaci duk kungiyar Premier da ke son karbar aron Philippe Coutinho ta biya ta £9m. Za a sayar da dan wasan na Brazil, mai shekara 27, a kan £71m. (Mundo Deportivo via Mirror)

Dan wasan tsakiya na Atletico Madrid wandaManchester United take son daukowa Saul Niguez ya ce nan da kwana uku masu zuwa zai "sanar da sabuwar kungiyarsa". Za a sayar da dan wasan na Spaniya, mai shekara 25, a kan £130m. (Manchester Evening News)

Ana sa ran Everton za ta dawo da golan Denmark Jonas Lossl, mai shekara 31, a karshen zaman aron da yake yi a Huddersfield Town. (Yorkshire Evening Post)

Celtic tana duba yiwuwar dauko golanManchester City da Chile Claudio Bravo, mai shekara 37. (Times - in Spanish)

KocinChelsea Frank Lampard ya ce zai yi "garanbawul" ga tawagar kungiyar idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo a bazara. (Mail)

Inter Milan ta ce tana so ta rike dan wasan da ta karbo aro daga Manchester United Alexis Sanchez fiye da wa'adinsa na ranar 30 ga watan Yuni. Da ma dai kungiyar ta karbo aron dan kasar ta Chile, mai shekara 31 ne zuwa karshen kakar wasa ta bana. (Sky Sports Italia via Talksport)