Chelsea tana son sayo Chilwell, har yanzu Zidane yana son ɗauko Pogba

Ben Chilwell

Asalin hoton, Getty Images

Chelsea ta ce babban abin da ta sanya a gaba yanzu shi ne dauko dan wasan Leicester Ben Chilwell, mai shekara 23, ko da yake za a sayar da dan wasan na Ingila a kudin da ya kai £85m. (Athletic - subscription required)

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi magana da wakilin dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekara 27, yana mai cewa har yanzu suna sha'awar dauko dan wasan na Faransa. (Le 10 Sport - in French)

Manchester United tana son karbo dan wasan Velez Sarsfield dan kasar Argentina Thiago Almada, mai shekara 19, a matsayin zabin da ya rage mata idan bata samu damar dauko dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20 ba. (Manchester Evening News)

Inter Milan za ta soma yunkurin dauko dan wasan Arsenal dan kasar Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 29, idan dan wasan gaba na Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, ya koma Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tottenham ta bai wa dan wasan Ingila Danny Rose, mai shekara 29, damar ci gaba da zaman aro a Newcastle zuwa karshen kakar wasan bana. (Football Insider)

Udinese ta yi tayin biyan £30,000 duk mako ga dan wasan Newcastle Matty Longstaff, dan shekara 20, wanda yanzu haka ake biyansa £850 duk mako, a yayin da Magpies suke son a ba su ladan £400,000 kan dan wasan. (Sky Sports)

Barcelona tana so ta sake dauko dan wasan Spaniya Eric Garcia, dan shekara 19, daga Manchester City. (ESPN)

Galatasaray ta bi sahun wasu kungiyoyi wajen yunkurin dauko dan wasan Charlton da Montserrat Lyle Taylor, mai shekara 30, wanda ya ce ba zai sake buga wa kungiyar tamaula ba idan kwangilarsa ta kare a bazarar nan. (Mail)

Da alama Brighton za ta gaza sayen dan wasan Rennes M'Baye Niang a kan £15m, don haka Marseille ta soma tattaunawa don dauko dan wasan na Faransa mai shekara 25. (Star)

Hukumar Gasar Premier ta gaya wa kungiyoyin da ke buga gasar cewa ba za a buga wasa fiye da hudu ba a filin 'yan-ba-ruwanmu, abin da hakan ke nufin Liverpool za ta iya lashe gasar ta Premier a filin Anfield. (Mail)